December 7, 2025

Mutanen gari a Sokoto sun yi kukan kura, sun nufi daji domin tunkarar ƴanbindiga

images (24)

Daga Sabiu Abdullahi

Mazauna garin Gobir a jihar Sokoto, sun yi kukan kura, sun nufi dazuzzuka domin tunkarar ‘yan bindiga da kuma kubutar da ‘yan uwansu da aka sace, saboda gazawar jami’an tsaro.  

Mazauna yankin da suka hada da maza da mata, sun shiga aikin ceto ‘yan uwan nasu 150 ne da aka yi garkuwa da su, tare da kwato gawar Hakimin Gobir Isa Mohammad Bawa da aka kashe, wanda ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla, bayan sun yi garkuwa da shi tare da azabtar da shi da kuma cin zarafinsa.  

Jaridar Sahara Reporters a Najeriya ta rawaito cewa matakin na zuwa ne bayan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta ikirarin sace mutane 150 da aka yi a masarautar Gobir ta jihar Sokoto.  

“Ba mu da labarin sace mutane 150 da aka yi a Masarautar Gobir ta Jihar Sakkwato,” in ji ASP Ahmed Rufa’i, Kakakin Rundunar ‘Yansandan Jihar Sakkwato.  

Sai dai Farfesa Bello Bada na Jami’ar Usman Dan Fodio Sokoto ya tabbatar da faruwar lamarin na garkuwa da mutanen da aka yi tsakanin kisan marigayi Sarkin da kuma ranar Juma’ar makon jiya.  

Matakin da mazauna yankin suka dauka na daukar al’amura a hannunsu ya nuna irin yadda al’ummomin da ke fama da matsalar ‘yan fashi ke ci gaba da tabarbarewa a Najeriya.