Mutane Sama da 50 Sun Rasa Rayukansu Bayan Ƙonewar Wata Tanka a Jihar Neja

Daga Sabiu Abdullahi
Mutane sama da 50 sun rasa rayukansu a wata mummunar gobarar tanka da ta faru a ranar Asabar a kan titin Dikko-Maje da ke Karamar Hukumar Suleja a Jihar Neja.
Wasu da dama sun jikkata yayin da suke kokarin kwashe man fetur da ya zube daga tankar da ta kife.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Neja, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Minna.
Ya bayyana cewa tankar ta kife ne tare da zubar da man fetur a kan hanya.
Ya kara da cewa, “Mutane sama da 50 sun rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.” Tsukwam ya kuma ce wadanda suka yi kokarin ceton rayuka sun faɗa cikin wutar.
Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba-Arah, ya bayyana cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 9 na safe yayin da ake kokarin kwashe man daga tankar zuwa wata mota.
Hukumar NSEMA, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da mazauna yankin sun dukufa wajen aikin ceto da gano gawarwaki.
Baba-Arah ya tabbatar da cewa an kai wadanda suka jikkata asibitoci, yayin da ake ci gaba da gano gawarwakin wadanda suka mutu. Ya kuma roki mazauna yankin su ba da hadin kai ga masu aikin agaji.
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Neja, Bologi Ibrahim, ya tabbatar da lamarin yayin da gwamnan ya kai ziyara wajen duba ayyuka a Suleja da Tafa.
Gwamna Mohammed Umaru Bago ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi taka-tsan-tsan tare da kiyaye matakan tsaro.
I do agree with all the ideas you have introduced on your post They are very convincing and will definitely work Still the posts are very short for newbies May just you please prolong them a little from subsequent time Thank you for the post HABANERO88
Hi, itts pleasant posat on tthe topc of medoa print,
we aall understabd media iss a impressiove source oof data.