May 17, 2025

Mutane Huɗu Sun Rasu, Wasu Goma Sun Ji Rauni a Hatsarin Mota a Jigawa

7364cf50-9d57-461b-8d19-4bdd3fd9352e.jpg.webp

Mutane huɗu sun rasu wasu goma kuma sun ji raunuka a sakamakon wata gobara da ta tashi a cikin wata motar bas (Hummer) a garin Gwaram, Jihar Jigawa.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma a ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandare ta haɗaka ta gwamnati ta ‘yan mata (Government Girls Unity Secondary School) da ke garin Gwaram.

A cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya fitar a yau Lahadi, ya bayyana cewa motar ta taso ne daga Ƙaramar Hukumar Zaki ta Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa.

Sanarwar ta bayyana cewa motar na ɗauke da fasinjoji 44, ciki har da manya 25 da yara 19.

Kakakin ‘yan sandan ya ce gobarar ta faru ne sakamakon wata katifa da aka ɗaure a bayan motar, kusa da bututun hayakinta.