Mutane da dama sun mutu a Nasarawa kan rikicin gona

Daga: Abdullahi I. Adam
Sakamakon wani rikici da ya ɓallle tsakanin al’ummun Alago da Tivi a ƙaramar hukumar Keana da ke jihar Nasarawa, rahotanni sun tabbatar da cewa an rasa rayuka da dama waɗanda a halin yanzu ba’a san adadinsu ba.
Rashin jituwar ya samo asali ne bayan da aka tarar da gawarwakin wasu ‘yan ƙabilar Alago a gonakinsu a makon da ya gabata, wanda hakan ya jawo mummunan martani daga ɓangarensu kan Tivi da su ke a yankin.
A martanin da gwamnatin jihar ta yi kan lamarin, ta bakin babban mai taimaka ma gwamna Abdullahi Sule kan lamuran al’umma, Peter Ehemba, gwamnatin ta yi Allah wadai da lamarin tare da iƙirarin cewa suna da tabbacin cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu su huɗu su ke jinya.
Shugaban ƙungiyar al’umman Tiv na jihar ta Nasarawa, Kwamared Simeon Apusu ya nuna rashin jin daɗinsa kan lamarin tare da kiran cewa a kai hankali nesa don ganin cewa irin hakan ba ta sake faruwa ba.
A zantawarsa da manema labaru jim kaɗan bayan wani taro na gaggawa da ya kira a Lafiya bayan faruwar lamarin, Apusun ya roƙi ɓangarorin da su sulhunta da juna.
A nata ɓarayin, rundunar’yansandan jihar ta Nasarawa ta nemi jama’a da su kwantar da hankulansu sannan ta tabbatar ma jama’a cewa lamarin bai fi ƙarfinsu ba. Babban jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a jihar, DSP Ramhan Nansel ya ce “tuni lamura su ka koma daidai bayan hatsaniyar, domin ‘yansanda na iya ƙoƙarinsu kan lamarin.” inji shi.