April 26, 2025

Mutane 5 sun rasa rayukansu sanadiyyar kifewar kwale-kwale a Jigawa

images (7) (18)

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa mutane biyar sun rasa rayukansu bayan kifewar kwale-kwale a yankin ƙaramar hukumar Taura ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar DSP Lawan Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an ‘yansadan da masu nutso da ƙwararrun ninƙaya na kan ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin da suka ɓace.

A cewar kafar BBC Hausa, lamarin ya faru ne da ranar Alhamis, lokacin da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji 20 ya kife yayin da yake ƙoƙarin tsallake kogin Gamoda a kusa da ƙauyen Nahuce.

Wannan dai ya faru ne watanni bayan wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya janyo asarar rayuka a yankin ƙaramar hukumar Tauran.