January 15, 2025

Mutane 3 sun rasu a wani gini da ya rufta a Legas

27
IMG-20240725-WA0003.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ta sanar da rasuwar mutane uku a safiyar yau Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa mamatan sun gamu da hatsarin ne yayin da su ke aikin gini a wajen da ke rukunin gidaje na Arowojobe da ke Maryland a Legas.

A bayanin da babban sakataren hukumar, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu, ya aike wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa, NAN ya sanar da cewa lamarin ya auku ne a gida mai lamba 13, Layin  Wilson Mba, Arowojobe Maryland, Legas.

A cewarsa “da misalin ƙarfe 3:49 na tsakar dare mu ka sami labarin ruftawar ginin. Jami’anmu sun garzaya wajen da misalin ƙarfe 3:58

“Mun duƙufa wajen zaƙulo waɗanda su ke ƙarƙashin ginin, inda mu ka taras da mutane uku matattu, mutum biyu an ceto su day ransu sannan an gano wani da ya maƙale cikin ɓaraguzai”

A yanzu haka jami’an gwamnati waɗanda su ka haɗa da ‘yansanda da jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar suna wajen domin tabbatar da an ceto sauran mutanen da ake tsammani su na cikin ginin tare da tabbatar da tsaro a wajen.

27 thoughts on “Mutane 3 sun rasu a wani gini da ya rufta a Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *