January 15, 2025

MURIC ta yaba wa gwamnatin tarayya saboda ƙin amincewa da digiri na Benin da Togo

0
images-2024-01-04T202303.229.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa dakatar da karbar takardar shaidar digiri daga jamhuriyar Benin da Togo.

Farfesa Ishaq Akintola, Babban Darakta na MURIC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

“Abin yabawa ne da gwamnatin tarayya ta yi a lokacin da ta dakatar da amincewa da takardar shaidar digiri daga jamhuriyar Benin da Togo saboda rashin bin ka’ida da kuma ayyukan damfara,” in ji shi.

Gwamantin dai ta yi wannan dakatarwar ne sakamakon wani rahoton ƙwaƙwaf da wani ɗan jarida ya yi game da yadda ake bayar da takardar digiri a Benin ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *