Mun magance cinkoso a gidajen mai, inji NNPCL
Daga Abdullahi I. Adam
A yammacin jiya Alhamis ne kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, ya sanar da cewa matsalar dogayen layuka da ake fama da ita a gidajen mai ta kawo ƙarshe sakamakon irin matakan da kamfanin ke iƙirarin ya ɗauka kan lamarin.
Kamar yadda bayanai ke nunawa a cikin makonnan mai ƙarewa, cinkoso ya mamaye da dama daga cikin gidajen mai a ƙasar wanda har ya sanya wasu gidajen man ƙara farashin man zuwa ₦800 zuwa sama.
Kamar yadda kamfanin ya ambata a sanarwar, “rashin man ya taso ne saboda matsaloli da ke da nasaba da jigilar man” wanda ya ci karo da cikas a ‘yan kwanakinnan.
Har ila yau, kamfanin ya bada tabbacin cewa kwata-kwata ba shi da shirin yin ƙari a farashin man kamar yadda wasu ke yaɗawa.