January 24, 2025

Mun kashe ƴan ta’adda sama da 6,000 a 2023—sojojin Najeriya

9
IMG-20231229-WA0031.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A shekarar 2023 ne sojoji suka gudanar da ayyuka daban-daban a fadin kasar inda suka kashe jimillar ‘yan ta’adda 6,886 da sauran masu aikata laifuka.

Har ila yau, an kama jimillar mutane 6,970 da ake zargi da kuma kubutar da ‘yan kasar 4,488 da aka yi garkuwa da su.

Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Buba Edward ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan ayyukan sojojin a fadin kasar nan a shekarar 2023.

Ya kara da cewa, kokarin da sojojin suka yi a wannan shekarar ya kai ga kwato lita miliyan 100 na danyen man fetur da aka sata da kuma lita miliyan 60 na dizal.

An naƙalto Buba yana cewa, “A cikin wannan lokaci, sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 6,886 da sauran masu aikata laifuka. Sojoji sun kama mutane 6,970 da ake zargi, sun ceto mutane 4,488 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato makamai iri-iri 3,320 da alburusai 39,075.

Da yake yin nazari kan barazanar da aka fuskanta a shekarar 2023, Buba ya nuna cewa, ‘yan fashi, ta’addanci, garkuwa da mutane, satar mai, tayar da kayar baya, da rikicin manoma da makiyaya ne ke kan gaba.

9 thoughts on “Mun kashe ƴan ta’adda sama da 6,000 a 2023—sojojin Najeriya

  1. Pingback: cialis buy info/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *