Mun Kama Mutum 327 Kan Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba—Gwamnatin Najeriya
Daga TCR Hausa
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da cafke mutum 327 da ake zargi da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na kasar.
Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a lokacin bikin cika shekara guda da kafa rundunar Mining Marshals (MM), wadda ke kula da harkokin hakar ma’adanai.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito ministan yana cewa tun bayan kafa rundunar a 2024, an kama mutanen, inda aka gurfanar da 143 daga cikinsu a kotu.
Ya kara da cewa a 2025, babban abin da za su fi mayar da hankali akai shi ne tabbatar da gurfanar da sauran mutanen da aka kama.
A cewar NAN, an kaddamar da rundunar MM a ranar 21 ga watan Maris na 2024, inda ta fara aiki da dakaru 2,220, kafin daga baya yawan dakarun ya karu zuwa 2,670.




