Mun dakatar da shirin hana masu layin Glo kiran masu layin MTN—NCC

Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar sadarwa ta Najeriya (watau NCC a taƙaice) ta samar da dakatar da shirinta na hana masu amfani da layin Glo kiran mutane masu amfani da layukan MTN na tsawon kwanaki ashirin ɗaya.
Daraktan hulda da jama’a na hukumar NCC, Reuben Mouka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
A cewarsa, hukumar ta fasa kaddamar da matakin ne bayan da kamfanonin sadarwar suka yadda da warware duk matsalolin da ke tsakaninsu.
Idan mai ƙara bai manta ba, hukumar ta tabbatar da cewa ta amince da kamfanin MTN ya fara yanke kira da layin kamfanin Glo daga ranar 18 ga Janairu, 2024, saboda takaddamar bashin da ya daɗe a tsakanin ɓangarorin.
BBC Hausa ta ambato sanarwar tana cewa, “Hukumar ta yi farin cikin sanar da cewa a yanzu kamfanonin MTN da Glo sun cimma matsaya don warware duk wata matsala da ke tsakaninsu, saboda haka, hukumar ta dage dakatarwar da aka yi na tsawon kwanaki 21 daga yau 17 ga Janairu, 2024.
“A wajen bayar da amincewar hukumar, hukumar tana sane da illolin da shawarar za ta iya haifarwa ga masu amfani kamfanonin sadarwar biyu, don haka ta ci gaba da jan hankalin bangarorin biyu don saukaka wani kuduri wanda ya ba da fifiko da kuma kare muradun mabukaci da kuma tafiyar da harkokin sadarwa ta kasa baki daya,” in ji NCC.
“Yayin da hukumar ke sa ran MTN da Glo za su warware duk wata matsala da ta kunno kai a cikin kwanaki 21, hukumar ta ce dole ne duk kamfanonin da ke aiki su warware basussuka a matsayin wani abin da ya dace don bin ka’idojin doka na duk masu lasisi.”