Mun daƙile harin da Iran ta kawo mana—Isra’ila

Wallafar BBC Hausa
Sojojin Isra’ila sun ce sun yi haɗaka da wasu ƙasashe wajen daƙile gomman harin makamai masu linzami da Iran ta kai mata.
Wannan bayani martani ne ga harin makami mi linzami ta sama da Iran ta kaddamar kan Isra’ila.
Karon farko kenan da ƙasashen biyu zasu yi amfani da ƙarfin soji a kan juna, bayan shafe shekaru ana nuna yatsa da kuma yarfe ga juna.
Tuni dai firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya kira taron majalisar ƙoli ta yaƙin ƙasar domin tantance mataki na gaba.
Dama dai Iran ta sha alwashin kai harin ramuwa kan Isra’ilan, tun bayan wani hari da aka kai ofishin jakadancin ta da ke Syria, a ranr ɗaya ga watan Afirelu.
Iran ta zargi Isr’ila da kai harin, wanda ya kashe wani babban kwamandan rundunar juyin juya hali, sai dai Isra’ilan ta ce bata da hannu a harin.
A wani jawabi, kakakin rundunar tsaron Isra’ila, Rear Admiral Daniel Hagari ya ce dakarun su da gamayyar ƙawayen su sun yi nasarar daƙile ɗaruruwan makami mai linzami da Iran ta harbo.
Ya ce an samu wajen da wasu makaman suka fada, a cikin Isra’ila, amma basu kashe kowa ba.
Jami’an gwamnatin Amurka da na Birtaniya ma duk sun tabbatar da cewa dakarun ƙasashen su sun taimaka wajen daƙile harin na sararin samaniya.
Shugaba Biden na Amurka ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyar G7 a yau Lahadi domin tattauna matakan da ya kamata a ɗauka kan batun.