Mummunar gobara ta laƙume shaguna 180 a kasuwar Sokoto
Daga Sabiu Abdullahi
Gobara ta yi barna a babbar kasuwar jihar Sokoto da safiyar yau Litinin inda ta yi sanadin ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna.
Shugaban ƴan mashin reshen jihar, Garba Muhammad Gwazi, ya bayyana cewa gobarar ta laƙume shaguna ‘180’ na masu sayar da mashin.
Ya ƙara da cewa har yanzu ba a san abin da ya janyo tashin gobarar ba da ta janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira.
Sai dai BBC ta rawaito cewa gobarar ta soma ne daga wata shara da aka tara.




