January 15, 2025

Mokhbar zai ɗare shugabancin Iran

1
IMG-20240520-WA0019.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Kamar yadda sashe na 131 na kundin tsarin mulkin jamhuriyar ta Musulunci ta Iran ya tanada idan an sami mutuwar shugaba, mataimakin shugaba na ɗaya “tare da sahalewar jagorancin ƙasar, shi ne zai gaje shi, sannan daga bisani majalisar da ke ƙunshe da kakakin majalisar da shugaban sashen Shari’a da kuma mataimakin shugaban na farko za su shirya zaɓen sabon shugaban ƙasa, cikin kwanakin da ba su wuce 50 ba.”

Jagoran addini na Irin Ayatollah Khamenei ne ya tabbatar da rasuwar sannan ya sanar da cewa mataimakin shugaban na ɗaya, Mohammad Mokhbar Dezfuli ne zai gaji kujerar shugabancin ƙasar kafin gudanar da zaɓe.

Daga yanzu har zuwa lokacin da za’a gudanar da zaɓe a ƙasar, Mokhbar ne zai cigaba da riƙe madafun iko a ƙasar kamar yadda tsarin mulkin Iran ɗin ya tanada.

Mohammad Mokhbar Dezfuli ya taɓa zama  shugaban ma’aikatan Farman Imam, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin masu ƙarfin tattalin arziki a jamhuriyar Musulunci ta Iran, na kusan shekaru 15 tun kafin zamowarsa mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya.

1 thought on “Mokhbar zai ɗare shugabancin Iran

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *