January 15, 2025

Ministan tsaro ya kuma buƙaci hafsoshin tsaro su koma Arewa maso Yamma

0
IMG-20240831-WA0027

Daga Sabiu Abdullahi  

Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana bakin cikinsa dangane da ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ke addabar jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, da Kebbi.  

Domin magance hakan ne ma ya sa Dakta Matawalle ya umurci Hafsan Hafsoshin Soji da sauran hafsoshin soji da su koma Sokoto, hedkwatar GOC, domin kara zage damtse wajen kawar da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.  

Dakta Matawalle ya bayyana cewa, “A shirye muke mu tura duk wasu abubuwan da suka dace domin ganin an kawar da masu aikata waɗannan miyagun laifuka tare da samar da zaman lafiya a cikin al’ummarmu.”

Ya bayyana cewa, tsaro da jin dadin jama’a shi ne babban abin da gwamnati ta sa a gaba.  

Ministan ya kuma yi kira ga al’ummar jihohin da abin ya shafa da su sanya ido tare da ba jami’an tsaro hadin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *