March 28, 2025

Ministan shari’a ya nuna yiwuwar watsi da tuhumar cin amanar ƙasa da aka yi wa ƙananan yara bayan ce-ce-ku-ce

images-28.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, ya fara daukar matakan watsi da tuhumar da aka yi wa yara 32 da aka gurfanar gaban Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
 
Yaran suna daga cikin mutane 119 da ake tuhuma da laifin shiga zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agusta.
 
Bayan gurfanar da su a kotu, Fagbemi ya bayyana sha’awar karbar alhakin shari’ar daga hannun Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, yana mai cewa akwai wasu abubuwan da ofishinsa zai yi nazari a kansu.
 
“Akwai wasu batutuwa da ofishina zai duba dangane da wannan batu domin samun damar yanke shawara bisa sanin makamar aiki,” inji shi.
 
Fagbemi ya umurci ‘yan sandan Najeriya da su mika takardun shari’ar zuwa ofishinsa, sannan ya nemi Daraktan Gabatar da Kara na Tarayya ya dauki matakan samo ranar shari’a da wuri.
 
Wata majiya daga Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta tabbatar da cewa an mika takardun shari’ar, kuma ana cikin shirin watsi da tuhumar.
 
 

2 thoughts on “Ministan shari’a ya nuna yiwuwar watsi da tuhumar cin amanar ƙasa da aka yi wa ƙananan yara bayan ce-ce-ku-ce

Comments are closed.