May 17, 2025

Messi Na Iya Ƙaurace Wa Wasansu Da Sporting Kansas City Saboda Tsananin Sanyi

1200-L-fc-barcelone-psg-lionel-messi-rvle-son-dernier-dfi-1.jpg

Shahararren ɗan wasan Argentina, Lionel Messi, wanda ke taka leda a Inter Miami ta Amurka, ana hasashen ba zai buga wasan da ƙungiyarsa za ta kara da Sporting Kansas City ba a ranar Talata mai zuwa.

Wasan, wanda zai gudana a filin wasa na Sporting KC da ke jihar Kansas, na ɗaya daga cikin wasannin buɗe gasar Zakarun CONCACAF na nahiyar Amurka. Sai dai hasashen yanayi ya nuna cewa yanayin sanyi mai tsanani zai sauka a ranar, inda zai iya kaiwa -24C saboda iska mai ƙarfi.

Rahotanni sun bayyana cewa Messi yana kokwanto kan buga wasan, kasancewar ya saba da yanayin zafi a kudancin Florida, inda Inter Miami ke da sansanin wasanta. Wani rahoton ya nuna cewa filin wasan na Sporting KC zai sami -15C a ma’aunin Celcius, amma iska za ta sanya jin kamar -24C.’ ne.

Ana iya jinkirta wasan

Wasu rahotanni sun nuna cewa ana tattaunawa kan yiwuwar jinkirta wasan ko sauya filinsa zuwa wuri da ke da sauƙin yanayi. Wani ɗan jarida da shafin Goal ya ambato, Franco Panizo, ya bayyana cewa Messi ba ya fatan zuwa wannan wasan.

A cewarsa, “Wasu majiyoyi sun gaya min cewa Lionel Messi ba ya son buga wasan na Talata cikin matsanancin sanyi tare da Sporting KC. Ko zai je ko ba zai je ba, za a jira a tabbatar, amma akwai yiwuwar ba zai buga wasan buɗe gasar Zakarun CONCACAF ba.”

Haka kuma, abokin wasan Messi a Inter Miami, Luis Suarez, ya taɓa bayyana cewa Messi ba ya son sanyi. A cewarsa, “Ya gaya min cewa yana shan wahala sosai a lokacin sanyi da ƙanƙara.

17 thoughts on “Messi Na Iya Ƙaurace Wa Wasansu Da Sporting Kansas City Saboda Tsananin Sanyi

Comments are closed.