Matsin rayuwa ya ƙara jefa matasa cikin ta’addanci, inji sojin Najeriya
Daga Abdullahi I. Adam
A wani taro da sojin na Najeriya suka gabatar don bikin murnan cika shekara ɗaya da hafsan tsaro na ƙasa, Christopher Musa, ya yi a kan karaga, daraktan watsa labarai na rundunar sojin Najeriyar Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana cewa ana samun ƙaruwan matasa da ke ɗaukan makamai saboda irin hali na matsi da ake fama da shi a faɗin ƙasar.
Kamar yadda Birgediya Janar Gusau ɗin ya bayyana, wannan matsala ce da ke maida hannun agogo baya a yaƙin da ake yi da matsalolin tsaro a faɗin Najeriyar.
Burgediyan ya bayyana ma kafar sadarwa ta BBC Hausa cewa, ”bai kamata matashi ya shiga irin wannan aiki na saɓa doka ba, sabida wani hali da ya tsinci kansa a ciki,” a cewarsa.
Birgediya Gusau ya kuma koka kan rashin isassun makamai da sauran kayan aiki da su ke fama da shi duk da cewa ya jinjina ma gwamnati kan irin ƙoƙari da ta ke na ware kuɗaɗe ga ɓangaren na tsaro wanda a cewarsa ana buƙatar ƙari don cimma nasaran da ake buƙata.
Rundunar sojin ta ce duk da matsaloli da ake fuskanta, akwai nasarori da dama da aka cimma a shekara guda ta farko da shugaban rundunonin tsaron ƙasar ya yi a kan mulki.
Sojin na Najeriya sun ce, “a bara hanyar da ta taso daga Abuja zuwa Kaduna, kusan kullum sai ka ji an yi garkuwa da mutane, amma yanzu saboda matakai da mu ke dauƙa an magance wannan matsala, mutane na bin hanyar ba tare da wata fargaba ko matsala ba.” inji rundunar.
Duka wannan na zuwa ne daidai lokacin da wasu da dama a yankin arewacin Najeriyar ke ganin harkar tsaro a ƙasar na ƙara taɓarɓarewa ne, wanda ko a farkon watan nan na Yuni, wasu ƴan majalisar wakilan kasar na Arewa, inda aka fi fama da matsalar tsaron sun tayar da jijiyar wuya, suna kiran a sauya salon yadda ake yaƙi da matsalar, domin a ganinsu babu wani sauƙi da ake samu.