January 14, 2025

Matsalar tsaro ta tilasta wa jama’a gudanar da zanga-zanga a fadar Zazzau

3
IMG-20240117-WA0003.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Al’ummomi daga yankunan Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar lumana a Fadar Maimartaba Sarkin Zazzau, Amb. Ahmad Nuhu, Bamalli a ranar Talatan nan.

Masu zanga-zangar sun fito ne daga yankunan da suka ƙunshi Galadimawa, Fatika, Kidandan da wasu yankuna na ƙaramar hukumar.

A wajen zanga-zangar, an ga matasa ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonnin irin halin rashin tabbas da yankin ke ciki na rashin tsaro.

Ko a cikin makon da ya gabata, mun sami rahotanni kan irin ɓarnar da maharan suka yi a wani yankin Tumɓurku mai suna Hayin Teacher inda suka hallaka aƙalla mutane biyu da yin awon gaba da wasu mutanen da dama.

Ƙaramar Hukumar Giwa na fama da matsalar hare-haren ‘yan ta’addan daji wanda lamarin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a cikin shekarun nan.

3 thoughts on “Matsalar tsaro ta tilasta wa jama’a gudanar da zanga-zanga a fadar Zazzau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *