January 14, 2025

Matashin da ya halaka kansa bayan ya yi asarar miliyoyi naira a caca

4
Mr-Onoh-the-victim-720x570.jpg

Wani mutum mai shekaru 31 ya kashe kansa a jihar Abia, a kudu maso gabashin Najeriya, bayan da aka ce ya yi asarar naira miliyan 2.5 a wata caca da ya yi ta yanar gizo.

Mutumin mai suna Chukwuma Onoh an ce ya ciyo bashin naira miliyan 1.2 daga hannun abokansa inda ya hada da naira miliyan 1.3 don yin cacar, amma bai yi nasara ba.

An ce ya tura wani sakon WhatsApp, yana roƙon wani mutum da aka ce shi ne maigidansa da ya taimaka ya biya masa bashin naira miliyan 1.2 da ya ci bayan ya yi asarar naira miliyan 2.5.

Sai dai mutumin ya ce masa ba shi da kuɗin da zinariya wannan bashin.

4 thoughts on “Matashin da ya halaka kansa bayan ya yi asarar miliyoyi naira a caca

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *