Matashi ya kashe ‘yar shekara 6 a Zaria
Daga Abdullahi I. Adam
Rundunar ‘yansandan Nigeria shiyyar Kaduna ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi inda take bayyana cewa dakarunta sun sami nasarar damƙe wani matashi mai suna Abdulazeez Idris wanda ake zargi cewa ya hallaka wata yarinya ‘yar shekara 6 a Zaria.
TCR Hausa ta sami labarin cewa mahaifin yarinyar, Mal. Saidu Dahiru, da ke Unguwar Juma a birnin Zaria, ya bayyana ma hukumomi cewa ‘yarsa mai shekaru 6 mai suna Aisha Dahiru ta ɓata kuma an neme ta ba’a ganta ba tun bayan fitarta makarantar islamiyya.
Mal. Saidu ya zargi cewa Abdulazeez ne ya yi garkuwa da ‘yar ta sa, duk da cewa, Abdulazeez ɗa ne a wajensa, kuma zagin nasa ya biyo bayan wani kira ne da aka masa a waya inda ake neman da ya biya naira miliyan takwas don kuɓutar da ‘yar tasa daga hannun masu garkuwa da mutane.
A sanarwar da rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta fitar ta hannun mai magana da yawunta ASP Mansir Hassan, rundunar ta bayyana cewa matashin ya zo hannu, kuma ya ƙara da cewa “a halin yanzu sashen kula da laifukan garkuwa da mutane na bincike a kan lamarin.”
Matsahin ya bayyana cewa ya yi amfani da reza ne wajen yanka yarinyar sannan ya jefa ta a rijiya don tsoron kar ta bayyana shi domin ta gane shi.
Kwamishinan ’yan sandan Kaduna, CP Audu Ali Dabigi, ya tabbatar da cewa za’a bibiyi lamarin kuma za’a gurfanar da matsahin gaban ƙuliya manta-sabo da zarar jami’ansa sun kammala bincike kan lamarin.
вывод из запоя на дому ростов недорого http://www.vyvod-iz-zapoya-rostov12.ru .