Rashin aikin yi ya sa matashi ya ƙona takardun makarantarsa ƙurmus

Daga Sabiu Abdullahi
Alvin Ilenre, wanda ya kammala karatunsa a fannin Tarihi da Nazarin Kasa da Kasa daga Jami’ar Ajayi Crowther ta Jihar Oyo, ya dauki wani mataki mai tsauri na nuna rashin amincewa da matsalar rashin ayyukan yi da cin hanci da rashawa a Najeriya.
A cikin wani faifan bidiyo, an ga Ilenre yana kona takardun shaidar karatunsa da suka hada da digirinsa, kammala makarantar firamare, da takardar shaidar bautar kasa.
Jaridar Citizen Reports ta tattaro cewa Ilenre ya bayyana dalilan yanke hukuncin, yayin da ya ce bai da aikin yi tun watan Fabrairun 2022, kuma ya fuskanci kalubale da dama wajen neman aiki, duk da kasancewar ya kammala karatunsa.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa da yadda cin hanci da rashawa ke yaduwa a kasar, wanda a ganinsa ya ke hana ƙwararrun mutane samun ayyukan yi.
“Na kona takadduna saboda ina fama da wasu abubuwa kuma ina buƙatar rufa wa kaina asiri. Shi ya sa na kona su,” in ji Ilenre.