Matashi a Kano Ya Bayyana Yadda Ɓarayi Suka Shiga Gidansa Suka Yashe Shi

Wani matashin mai suna Abubakar ya bayyana yadda barayi suka farmaki gidansa da misalin karfe 3 na dare shekaranjiya, inda suka kwace masa kudi da kayayyakin kudi.
A cewar wanda abin ya faru da shi, ya ji motsi a gidan, hakan ya sa ya leko falo. Lokacin da ya leka ta taga, sai ya hango wani mutum yana tahowa kofar dakinsa.
Da ya motsa kofar dakin, sai maimakon barayin su gudu, daya daga cikinsu ya fara kiran sauran cewa su hanzarta su karaso. Kafin a yi wani yunkuri, sai suka leka ta taga suna barazanar harbe shi idan bai bude ba.
Abubakar ya ce, “Nace musu akan me? Me nai musu da zasu harbeni juyawar da zan yi nakoma uwar daki don dakko wayata suka daki ƙofar dakin cikin second ɗaya sai gasu a kaina da muggan makamai.”
Ya ƙara da cewa, “Suka ce na kwanta bayan na kwanta suka daure min hannu na tabaya agaban yarana.
“Suka ce aiko su aka yi su kashe ni. Yanzu na ba su ƙudi na fanshi kaina. Haka suka dinka yi min barazana.
“Suka takura matata sai da ta ɗauko musu duk abinda suke buƙata. Sun tafi da mashin dina da wayata Google Pixel 7 pro [wadda ta fi N600,000] da wayar matata OPPO da wayar almajirina Vivo. Kuma duk saida suka takura muka cire Pin din wayoyin.”
Haka nan, sun tafi da takalmasa, da power bank, da kuma kudi har N510,000-N450,000 na kasuwancisa da N60,000 na matarsa.
Abubakar ya koka da cewa, “Tabbas mun gamu da jarabta ta rayuwa. Sun gama kassarani ta ko ina. Allah ya bani hakkina cikin gaggawa.”
TCR ta yi ƙoƙarin tuntubarsa amma har yanzu ba mu samu amsa daga gare shi ba.