January 13, 2025

Matasa sun yi dirar mikiya kan tirelar BUA, sun wawashe taliya

0
IMG-20240302-WA0019.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Rahotanni daga Zariar Jihar Kaduna sun tabbatar da cewa wasu matasa sun far ma wata tirela ta kamfanin BUA wacce ta ke cike maƙil da taliya a kan babban titin Zaria zuwa Kano.

Lamarin wanda ya faru da tsakar ranar Juma’a jiya, ya faru ne sa’ilin da direban motar ya dakata domin sallar Juma’a a Dogarawa da ke Zaria.

A lokacin da ake tsaka da kwasan kayan, an ga mutane na ta jigilar taliyar don ɓoyewa da zimmar yin amfani da ita wanda lamarin ya fuskanci suka matuƙa daga jama’a mabambanta.

Bayan afkuwar lamarin, al’umma da dama sun alaƙanta afkuwar abin da yanayin matsi da jama’a ke fama da shi tun bayan cire tallafin mai da aka yi a ‘yan watannin da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *