March 28, 2025

Matasa sun hallaka wanda ake zargin ya yi ɓatanci ga Fiyayyen Halitta a Bauchi

IMG-20240428-WA0010.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kisan wani matashi mai suna Yunusa Usman da wasu fusatattun mutane suka yi a garin Nasaru da ke karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi a ranar Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa Yunusa dukan tsiya har sai da ya mutu sakamakon kalaman batanci da ake zargin ya yi wa Annabi Muhammadu S.A.W.

Lamarin dai ya janyo cece-kuce tsakanin mazauna garin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin, kuma ya tabbatar da cewa Yunusa na da hannu wajen yayata bayanai game da wani sabuwar akidar addini da aka fi sani da kungiyar Faira, wanda ya haifar da tashin hankali, kuma a karshe ya kai ga mutuwarsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad, ya yi kakkausar suka ga abin da mutanen da abin ya shafa suka aikata, ya kuma jaddada muhimmancin bin doka da oda, inda ya bukaci jama’a da su hada kai da jami’an tsaro su guji daukar doka a hannunsu.

Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, Yunusa dan kungiyar Islamic Faira ne kuma an ji shi yana zagin Manzon Allah, wanda hakan ya sa suka yi arangama da wasu matasa suka kalubalance shi da ya janye maganarsa.

“Lokacin da ya ƙi, sai suka fara dukansa, kuma duk da kokarin da jami’an ‘yan sanda suka yi na kubutar da shi, mutanen sun ci karfinsu,” inji shaidar.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa jama’a cewa an daidaita al’amura a yankin da lamarin ya shafa tare da kara sanya ido don tabbatar da tsaro da tsaron daukacin mazauna yankin.

An yi kira ga al’umma da su kwantar da hankulansu su gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.

349 thoughts on “Matasa sun hallaka wanda ake zargin ya yi ɓatanci ga Fiyayyen Halitta a Bauchi

  1. диплом о среднем профессиональном образовании где купить [url=https://server-diploms.ru/]диплом о среднем профессиональном образовании где купить[/url] .

  2. вывод из запоя круглосуточно нижний новгород [url=www.stranaua.ukrbb.net/viewtopic.php?f=2&t=59798/]вывод из запоя круглосуточно нижний новгород [/url] .

Comments are closed.