Matasa sun fusata sun afka wa ƴan bindiga lokacin da suka kawo hari a Sokoto
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto ta tabbatar da kashe mutum daya a yayin da matasan wani yanki a Sokoto suka far wa ‘yan bindiga lokacin wani farmaki da suka kai musu a ranar Asabar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Ahmad Rufa’i, ya ce ‘yan bindigar a lokacin da suke yunkurin kai farmaki a unguwar Kwakwala a cikin babban birnin Sakkwato, sun yi artabu da matasan yankin.
Rufa’i ya ce, “Bisa rahoton da muka samu, ‘yan bindigar da ake zargin sun kai kimanin 10 dauke da manyan bindigogi da kuma bindigogin Dane sun kai hari a wata unguwa da ke bayan babban harabar jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.
“Matasan yankin sun nuna turjiya wa hare-haren kuma ana cikin haka ne ‘yan bindigar suka harbe daya daga cikin matasan mai suna Usman wanda ya mutu nan take. Haka kuma wasu matasa hudu na al’ummar Kwalkwala da Dundaye sun samu raunuka daban-daban a harin.”