Matasa a Kano sun gudanar da gagarumar zanga-zanga saboda kisar matashi da ƴan sanda suka yi

Daga Ɗanlami Malanta
Al’amura sun tsaya a birnin Kano tun misalin ƙarfe bakwai na safe yayin mutane suka rufe titin Kurma har zuwa Rijiyar Lemo don nuna fushinsu game da kisar wani matashi da suke zargin ƴan sanda sun yi.
An ga yadda jama’a suke ta karaɗa hotunan zanga-zangar a shafukan sada zumunta.
Me ya faru?
Wani ganau ya faɗa wa wakilin TCR Hausa cewa jiya da daddare ƴan sanda sun biyo wasu mutane da suke zargin yan daba ne, suka shigo anguwar Kurna suka yi harbe-harbe na kan-mai-uwa-da-wabi a kan jama’a, har ta kai ga sun kashe ɗaya ɗaga ciki, sun Jikkata mutum uku, tare da kama wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Wanda aka kashe din tela ne kuma dan kwallon kafa amma kwatsam aka ji ƴan sanda sun sanar cewa sun lashe
Sai dai shaidun gani da ido sun musanta kuma sun bayyana wanda aka kashe din ko sigari ba ya sha.
Sanarwar da jama’ar gari suke ikirarin yan sanda fitar ne ya harzika jama’ar inda suka fito zanga zanga
Wani rahoto da yake fitowa kuma yan nuna cewa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya ba da umurnin kama ɗan sandan da ake zargi ya yi kisar.