Matar Sarkin Bichi ta faɗa hannun ƴan damfara
Daga Ɗanlami Malanta
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki ƙasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da Wani mutum mai suna Umar Bello Sadiq a gaban Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Zuwaira Yusuf kan zargin almundahana da kudin da suka kai naira milyan 20.
Matar sarkin Bichi kuma surukar Sarkin Kano Hajiya Faridah Nasir Bayero ce ta kai ƙarar abokin kasuwancinta kan ikirarinta na damfararta kudin da ta zuba a matsayin jari.
Kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito, an gurfanar da Umar Bello Sadiq a gaban kotun tare da kamfaninsa mai suna Marula Global Links Ltd bisa zargin karɓan zunzurutun kudi naira milyan 20 daga hannun Hajiya Farida da sunan zuba hannun jari a kasuwancin ma’danai.
Wanda ake zargin dai ya musanta wannan ikirari a gaban kotun.
Lauyan mai gabatar da ƙara Sadiq Kurawa ya nemi kotun da ta daga ƙarar, a yayin da lauyan wanda ake zargi Shu’aibu Mu’azu ya miƙa buƙatar ba da belin wanda yake karewa.
Bayan Sauraron dukkan ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta bayar da belin wanda ake zargin a kan kudi naira 500,000 tare da kawo mutum biyu da za su tsaya masa bisa sharaɗin masu tsaya masan dole su kasance ƴan‘uwansa na jini.