Mataimakin shugaban ƙasar Iran Mohammad Zarif ya yi murabus
Daga Abdullahi I. Adam
Mataimakin shugaban ƙasar Iran Mohammad Javad Zarif ya yi murabus ba zato ba tsammani daga muƙaminsa a ranar Litinin, kwanaki 11 kacal da shiga majalisar ministocin shugaba Massud Pezeshkian.
A cikin wata sanarwa da Zarif ɗin ya wallafa a shafinsa na X, Zarif ya nuna rashin gamsuwa da yanayin da gwamnatin ke tafiya a kai yana mai cewa, “Ban gamsu da aikina ba, kuma na yi nadamar cewa na kasa cika abin da ake buƙata.”
Rahotanni sun ce murabus ɗin na Zarif na da nasaba da rashin jituwa kan zaɓen ministocin sabuwar majalisar ministocin Pezeshkian.
Bayanan da Zarif, ɗin ya yi sun yi ishara da cewa rashin jituwa kan zaɓen ministoci ne ya sa ya yanke shawarar.
A cewar DW, Zarif ya lura cewa aƙalla bakwai daga cikin ministoci 19 da aka zaɓa ba su ne aka zaɓa ba tun farko.
Zarif, wanda ya taɓa kasancewa babban jami’in diflomasiyyar Iran daga 2013 zuwa 2021, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar ƙasa da ƙasa ta 2015, ya kasance jigo a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Pezeshkian.
Ana sa ran shahararsa da gogewarsa za su taimaka a yunƙurin da sabuwar gwamnatin ke yi na dawo da tattaunawar nukiliya da rage gurgunta takunkumin tattalin arziki da aka ƙaƙabawa Iran.
Masu lura da al’amuran yau da kullun na sa ido sosai kan yadda shugaba Pezeshkian zai tafiyar da wannan koma baya yayin da gwamnatinsa ke kokarin daidaitawa da kuma aiwatar da manufofinta.