January 15, 2025

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda ya kashe kansa a Oyo

5
GBOLAHAN.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Gbolahan Oyedemi, ya kashe kansa a ranar Litinin a gidansa da ke Ogbomoso a jihar Oyo, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Oyedemi, wanda ya yi aiki da sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda a Alagbon, jihar Legas, an same shi a mace a gidansa

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Eh, ya kashe kansa ne, jiya (Litinin) aka tsinci gawarsa a rataye a gidansa, shi kadai yake zaune, kuma yakan dawo gida ne domin bikin Ista, a wannan karon ya shaida wa mukarrabansa su je su yi biki tare da ’yan uwa a gidajensu daban-daban, Allah ne kadai ya san abin da ya sa shi kashe kansa.”

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya ci tura domin har yanzu an kasa samun lambar wayarsa.

5 thoughts on “Mataimakin kwamishinan ƴan sanda ya kashe kansa a Oyo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *