Mata da miji sun lakaɗa wa wani mutum duka
Daga Muhammad Mahmud Aliyu
Wani miji da matarsa sun bayyana a gaban alƙaliyar kotun Kibera bisa zargin lakaɗa wa wani mutum duka.
Ana zargin Justus Mmera da matarsa Juliet Ouma wajen haɗa kai kan yi wa wani mutum dukan tsiya saboda ya tambayi matar game da lafiyar ɗanta.
Lamarin dai ya faru ne a ranar 19 ga watan Satumba na wannan shekarar, kamar yadda takardar shigar da ƙara ta nuna.
Geoffrey Okuku wanda shi ne mai shigar da ƙara, ya bayyana cewa ya haɗu da ma’auratan ne a kan hanya a unguwar Kawangware da ke Nairobi babban birnin Kenya.
Haɗuwarsu ke da wuya ya tambayi matar ya ɗanta yake. Su kuma tambayar ba ta yi musu daɗi ba, shi ya sa nan take suka rufe shi da duka.
Cif Majistare Ann Mwangi ta tambayi Justus matsayin Juliet a wajensa, inda ya bayyana cewa matarsa ce ta halal, amma dai ɗan na matarsa ne.
A ƙarshe alƙaliyar ta ba da belin su a kan kuɗi Shilin dubu goma (kimanin Naira dubu hamsin), tare da mai tsaya musu da shi ma zai ajiye adadin wancan kuɗin a wurin kotu.