January 15, 2025

Masu zanga-zangar #EndBadGovernance sun yi kira a yi yajin aiki da zanga-zanga saboda ƙarin farashin man fetur

0
IMG-20241010-WA0007.jpg

Daga Sabiu Abdullahi


Gungun masu fafutukar #EndBadGovernance a jihar Legas ya yi tir da tashin farashin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi kwanan nan, inda suka bayyana shi a matsayin “abubuwan da suka tayar da hankali da ba za a iya yarda da su ba.”

Jama’ar sun bayyana wannan karin farashi a matsayin wata matsala ga ‘yan Najeriya da ke fama da wahala.

A cikin wata sanarwa mai taken “Tashin Farashin Mai Na Karshe Ya Nuna Shugaba Tinubu Bai Gama Da Mu Ba,” sun bukaci a janye wannan karin farashin nan take kuma sun bukaci ‘yan Najeriya su yi zanga-zanga kan wannan lamari.

Sanarwar da Hassan Taiwo Soweto, Osugba Blessing, da Oloye Adegboyega-Adeniji suka sanya wa hannu ta ce wannan karin farashi zai kara jefa ‘yan Najeriya cikin yunwa da tsananin talauci.

A cewar rahotanni daga kafofin watsa labarai, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya kara farashin fetur zuwa tsakanin N998 a kowanne lita a Legas da kuma N1,030 a Abuja da sauran sassan kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *