Masu sayar da jarida sun koka kan yadda jaridun yanar gizo suka ‘kashe musu kasuwa’
Daga Sabiu Abdullahi
Masu sayar da jarida a jihar Osun na kokawa kan yadda za su ci gaba da rayuwa sakamakon yawaitar kafafen yada labarai na yanar gizo, lamarin da ya sa aka rage sayen kwafi-kwafi na jaridu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Oladayo Salau, wani mai sayar da jaridu a Old Garage, Osogbo, ya ce “Kasuwar jaridu a kwanakin nan ta yi muni matuka, kuma saboda labaran da za su fito a jarida a washegari sun riga sun shiga yanar gizo kwana guda kafin nan.”
Ya kara da cewa, “Mutane yanzu suna kallon labarai a cikin jarida a matsayin tsohon labari. Ga masu sayar da kayayyaki irina, ba za mu sake samun kudi ba, sai dai wasu ‘yan kalilan da ke son canza sunayensu a jaridu.”
Kasim Madamudola, wakilin tallace-tallacen jaridu, ya ce ya daina sayar da jaridu tsawon wasu watanni saboda karancin kasuwar da yake samu.
“Yanzu mutane sun gwammace su yi amfani da wayoyinsu don samun bayanan da ake bukata maimakon sayen jaridu,” a cewarsa.
Wani mai sayar da jaridu, Shola Akiolu, ya ce yanzu mutane ba su damu da sayen jaridu ba tun lokacin da kafafen yada labarai na intanet suka bullo.
“Masu karatun jaridu sun fi son amfani da wayoyinsu domin samun labarai da bayanan da ake bukata,” in ji shi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da su ma kansu gidajen jaridun suke da shafukan yanar gizo domin buga kowane labari da ya zo da ɗumi-ɗuminsa.