Masu haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne suka haddasa fashewar bam a Ibadan—Gwamna Makinde
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar su ne suka jawo fashewar wani abu da ya faru a daren ranar Talata a Ibadan.
Gwamnan ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa masu hakar ma’adanan sun ajiye bama-bamai ne a daya daga cikin gidajen da abin ya faru.
A wata sanarwa bayan da ya ziyarci wurin da sauran asibitocin da wadanda suka jikkata ke karbar magani, Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu yayin da 77 suka jikkata kuma ana kula da su a asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu da ke kewaye.
Ya wallafa wannan bayanin ne a shafinsa na X da sanyin safiyar Laraba.
Ya ce, “Bincike na farko da jami’an tsaro suka gudanar ya nuna cewa masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da ke zama a daya daga cikin gidaje a Bodija, sun ajiye bama-baman a can ne har suka haddasa tashinsa. Ana ci gaba da gudanar da bincike. Duk wadanda aka samu da laifin haka za a gurfanar da su gaban kotu.”
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta biya kudin asibiti na wadanda suka jikkata, sannan ya kuma umarci dukkan otal-otal da su dauki wadanda suka rasa matsugunansu sakamakon fashewar.
вывод из запоя на дому ростов недорого https://vyvod-iz-zapoya-rostov12.ru .
капельница от запоя стоимость капельница от запоя стоимость .
Лечение от мефедрона в Казахстане https://www.narcologiya-kazakhstan.kz .
курс доллара в казахстане http://www.kursy-valut-online.kz .
моторное масло таиф http://e-taif.ru/ .
эскорт москва эскорт москва .
принудительное лечение от алкоголизма цена принудительное лечение от алкоголизма цена .
download instagram stories download instagram stories .