March 28, 2025

Masu amfani da layin MTN sun yi cincirindo a gaban ofishin kamfanin saboda katse musu layuka

images-6-10.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Wasu fusatattun masu amfani da layin MTN sun mamaye ofishin kamfanin MTN da ke Ibadan a jihar Oyo a safiyar ranar Litinin, inda wasu suka tayar da tarzoma tare da jifan ginin.
 
Zanga-zangar dai ta samo asali ne sakamakon matakin da kafar sadarwar ta dauka na toshe layukan masu amfani da wayar a ranar Lahadin da ta gabata, bisa zargin kasa haɗa Lambobin Shaida ta Kasa (NIN) da lambobin wayarsu.
 
Sai dai kuma wasu masu amfani da wayoyin da abin ya shafa sun yi ikirarin cewa da gangan ne kamfanin MTN ya yi haka.

A cewarsu, yana yunkurin dakile zanga-zangar kin jinin wasu kudurorin gwamnati da aka shirya yi ne a fadin kasar a ranar Alhamis.
 
“Al’amarin ya rikide zuwa tashin hankali, mutane na jifa da duwatsu,” wani ma’aikacin MTN ya bayyana yadda lamarin ya faru.
 
Har yanzu dai kamfanin sadarwar bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan takaddamar ba, inda ba a san adadin lambobin wayar da hakan ya shafa ba.
 
Ana sa ran za a yi irin wannan zanga-zanga a wasu sassan kasar a yau litinin, yayin da masu layukan waya ke nuna bacin ransu da yanke musu huldar kwatsam.