January 15, 2025

Manchester United ta naɗa Bruno a matsayin kyaftin

0
362007257_248664954618214_1607651358287537018_n

Ƙunigiyar kwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da naɗin ɗan kwallon ƙasar Portugal Bruno Fernandez a matsayin sabon kyaftin ɗin da zai jagoranci tawagar ƴan wasanta a kaka me zuwa.

Sanarwar ta biyo bayan tuɓe tsohon kyaftin ta kuma me tsaron bayan ƙungiyar Harry Maguire, bayan fama da koma-baya da rashin kataɓus a kakar da ta gabata.

Bruno Fernandez wanda ya fara taka leda a Manchester United a shekarar 2020, ya taka rawar gani a manyan wasannin hamayya da ƙungiyar tayi, tare da ci mata kwallaye da tallafi a mafi yawancin lokutan ƙaƙa-ni-kayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *