Malaman Jami’ar Jihar Gombe sun tsunduma yajin aiki a karon farko

Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Gombe (GSU) ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani, sakamakon gazawar gwamnatin jihar Gombe wajen biya musu bukatunsu.
Wannan dai shi ne karon farko da malaman jami’ar suka fara yajin aikin cikin gida tun kafuwar jami’ar.
Shugaban kungiyar ASUU, Suleiman Salihu Jauro, da sakataren kungiyar Mustapha Shehu, ne suka yi jawabi a taron manema labarai a jami’ar, inda suka danganta matakin da rashin aiwatar da yarjejeniyar aiki ta 2021 (MOA) tsakanin kungiyar da gwamnatin jihar Gombe.
MOA ta haɗa da ƙarin kudade ga jami’a, biyan kuɗin da aka tara na kudaden alawus na ilimi, da tsara kuɗin horo ga ma’aikatan ilimi.
Shugabannin kungiyar sun koka kan cewa gwamnatin jihar ta biya kudin da aka amince da shi ne kawai a watan Janairu da Fabrairun 2021, wanda hakan ke janyo karancin kudade da kuma matsi ga dalibai.
Sun bayyana cewa, ‘’Ya’yan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Gombe sun dade suna fama da tabarbarewar yanayin aiki a jami’ar.
“Kungiyar ta nemi a warware matsalolin cikin kwanciyar hankali ta hanyar neman sa hannun manyan mutane a jihar ba tare da wani sakamako mai girma ba.”