January 15, 2025

Malamai da ɗaliban jami’ar Gusau sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe wata 7 a hannun masu garkuwa da su

0
IMG-20240923-WA0012

Daga Abdullahi I. Adam

Ɗalibai da ma’aikatan Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke Jihar Zamfara, waɗanda ‘yanbindiga suka yi garkuwa da su, sun shaƙi iskar ‘yanci bayan watanni bakwai da suka yi a hannun masu garkuwa da su.

Su dai waɗannan malamai da ɗaliban nasu an yi garkuwa da su ne a wani hari da aka kai a yankin Gusau a watan Fabrairun wannan shekara.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma ƙwararre kan yaƙi da tada ƙayar baya, Zagazola Makama, ya tabbatar da hakan a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X a yau Litinin.

“Ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau da aka sace sun samu ‘yanci,” inji mai sharhin.

Duk da yake kawo yanzu ba a san haƙiƙanin halin da ake ciki na sakin su ba, majiyar Zagazola ta nuna cewa jami’an tsaro sun taka rawar gani wajen kuɓutar da su.

“An sami tabbacin yin garkuwa da ɗaliban da ma’aikatan a yayin wani hari da ‘yanbindiga suka kai a yankin Gusau a watan Fabrairun wannan shekara,” in ji Zagazola.

Labarin kuɓutar malaman da ɗaliban ya kawo kwanciyar hankali ga iyalai da sauran al’umma da suka daɗe suna jiran dawowar ‘yan’uwan nasu.

Zagazola ya ƙara da cewa, “Bayan an ɗauki tsawon lokaci ana garkuwa da su, an tabbatar da cewa dukkan mutan sun kuɓuta lami lafiya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *