Majalisun Najeriya za su ƙara cefanar da naira biliyan 30 domin kwaskwarima wa ginin majalisa
Daga Sabiu Abdullahi
‘Yan majalisun Najeriya sun ƙara kasafin kudi na naira biliyan 30 domin gyara ginin majalisar dokokin kasar a cikin kasafin kudin shekarar 2024.
Naira biliyan 30 ɗin da aka ware domin gyaran ginin na daga cikin naira biliyan 344.85 da aka ware wa majalisar dokokin kasar bayan da suka tara kason su daga naira biliyan 197.93.
Naira biliyan 344.85 da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 1 ga watan Janairu, ita ce mafi girma da aka taɓa ware wa majalisar.
Karin N30bn ya sa gaba ɗaya adadin kuɗin ya kai naira biliyan 60 matsayin kuɗaɗen da za a kashe wajen gyaran majalisar dokokin kasar.