January 14, 2025

Majalisar wakilai za ta kafa kwamiti don bincike ingancin fetur ɗin Dangote

10
IMG-20240722-WA0016.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

A wata ziyara.da majalisar wakilai ta ƙasa ta kai a matatar man fetur ta Dangote a Asabar ɗin nan, majalisar ta bayyana aniyarta na binciken ingancin man da matatar ta Dangote ke fiddawa.

Kamar yadda majalisar ta bayyana, binciken ya zama tilas ne saboda zargi da ake yi na cewa man da matatar ke tacewa bai da inganci.

Zargi ya yi yawa kan man na kamfanin Dangoten, wanda hakan ya tilasta majalisar aika wasu mambobinta ranar Asabar domin ziyarar matatar man tare da ganin yadda lamura ke gudana.

Shugaban majalisar Hon. Tajuddeen Abbas ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za’a kara wani ƙwaƙƙwaran kwamiti don gudanar da binciken, kuma za’a sanar da al’umma sakamakon binciken da zarar ya kammala.

Sai dai a nasa ɓangaren, shugaban matatar, Aliko Dangote,  ya tabbatar da cewa kayan man fetur da matatarsa ke samarwa suna da inganci kuma za’a iya amfani da su ko ina a ƙasashen duniya.

10 thoughts on “Majalisar wakilai za ta kafa kwamiti don bincike ingancin fetur ɗin Dangote

  1. Hello there! This is kind of off topic but I need some guidance from an established blog. Is it difficult to set up your own blog? I’m not very techincal but I can figure things out pretty quick. I’m thinking about creating my own but I’m not sure where to begin. Do you have any tips or suggestions? Many thanks
    фильмы 2024 смотреть онлайн

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *