November 8, 2025

Majalisar Wakilai Ta Umarci Sojoji Da Su Saki Shugaban Miyetti Allah, Bello Badejo

image_editor_output_image1779780815-1734500429985.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta bukaci a saki Shugaban Miyetti Allah, Bello Badejo, daga tsarewar da ta ce ba bisa ka’ida aka yi masa ba.

Haka kuma, majalisar ta gayyaci Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oloyede; da Kwamandan Runduna ta 177, don bayyana gaban kwamitocin majalisar na Sojoji, Kare Hakkin Dan’adam, da Shari’a.

Wannan kuduri ya biyo bayan wata kudiri da Hon. Mansur Soro ya gabatar, inda ya nuna damuwa cewa cafke Badejo a ranar 9 ga Disamba, 2024, a garin Maliya da ke Jihar Nasarawa, an yi shi ne ba tare da gayyata ko kuma umarnin kotu ba.

Soro ya bayyana cewa an ce cafkar ta shafi wata rashin jituwa tsakanin wani tsohon janar na soja da wasu al’ummar garin Maliya.

Majalisar ta yi Allah wadai da yunkurin jami’an runduna ta 177 na sojoji na kwace aikace-aikacen da ya rataya a hannun ‘yan sanda da kotu wajen warware rigingimu tsakanin ‘yan kasa.

Har ila yau, majalisar ta umarci sojojin su nemi afuwar Bello Badejo saboda take masa hakkokin sa na dan adam da kundin tsarin mulkin kasar ya tabbatar masa da su.

Tsare Badejo ya haifar da cece-kuce kan take hakkokin sa na dan adam da aka tanada a sassa na 34, 35, da 36 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, wanda aka yi wa gyaran fuska.