Majalisar wakilai ta ƙi amincewa da buƙatar Tinubu ta sayan jirgin ruwa wa fadar shugaban ƙasa
Daga Sabiu Abdullahi
Majalisar wakilai ta ki amincewa da kasafin N4.79bn na jirgin ruwan shugaban kasa da ke ƙunshe a cikin karin N2.176trn na kasafin kudin shekarar 2023 da shugaba Bola Tinubu ya miƙa mata ranar Talata.
A yayin zartar da ƙarin kasafin kudin a ranar Alhamis, majalisar ta mayar da kuɗaɗen da aka tanadar don jirgin zuwa rancen da za a a ba wa ɗalibai, wanda ya kawo jimillar kuɗaɗen shirin zuwa N10bn daga N5.5bn.
Abubakar Bichi, wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar a ranar Alhamis. “In dai don mu ne, ba ma buƙatar jirgin shugaban kasa kuma.
“Mun ƙara kuɗin rancen dalibai. Idan za a iya tunawa, bashin dalibai ya kai adadin N5bn a kasafin kudin, amma yanzu mun ƙara daga N5bn zuwa N10bn domin ɗalibanmu su samu damar shiga wannan wurin domin su samu damar zuwa makaranta su samu damar yin karatu,” in ji ɗan majalisar.
Bichi ya ƙara da cewa kwamitin ya ƙara wa ma’aikatar tsaro kasafin kuɗin daga kasafin da aka ware na N476bn zuwa N546bn.