January 14, 2025

Majalisar Najeriya za ta yi dokar kare haƙƙin ƴan aikin-gida

8
IMG-20240509-WA0004.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Majalisar dattijai a kasar nan, na shirin samar da dokar da za ta kafa hukumar tattara bayanai na ‘yan aikin-gida da kuma iyayen gidansu.

Majalsar ta ce za a samar da hukumar ne domin tabbatar da kare haƙƙin ‘yan aiki, waɗanda ke yawan fuskantar cin zarafi daga iyayen gidansu.

Kazalika, ƙudirin dokar ya tsallake karatu na biyu, ya nemi a kare iyayen gdan, waɗanda a wasu lokutan ke fuskantar hadari daga masu yi musu aikin.

“Idan ƙudirin nan ya zama doka to wajibi ne a bai wa ‘yan-aiki wurin kwana mai kyau kamar yadda mutum zai bai wa iyalinsa, ba za a ci mutuncinsu ba. Talauci ba zai zama hujjar da mutum zai mutuncin wani mutum ba,” in ji Sanata Babangida Hussaini.

8 thoughts on “Majalisar Najeriya za ta yi dokar kare haƙƙin ƴan aikin-gida

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *