January 14, 2025

Majalisar jihar Kano ta amince da ƙudirin kafa masarautu masu daraja ta biyu

1
IMG-20240716-WA0022.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

A safiyar yau Talata ne majalisar jihar Kano ta amince da ƙudirin kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar.


Idan ba’a manta ba, da ma chan majilisar ta kammala karatu na farko kan ƙudirin wanda ya sami amincewarta a yau kafin tafiya ɗan hutu da majalisar ta kammala a jiya.

A yayin da aka kammala karatu na biyu da na uku ga ƙudirin ne mataimakin kakakin majalisar, Hon. Muhammad Butubutu ya gabatar da ƙudirin amincewa da batun a zaman da majalisar ta gabatar bisa jagorancin kakakin majalisar Hon. Jibril Falgore.

Sabbin masarautu masu daraja ta biyun da za’a ƙirƙira su ne Bunkure da Kibiya daga masarautar Rano, sai Karaye da Rogo daga masarautar Karaye, sai kuma Gaya, da Ajingi  da Albasu daga masarautar Gaya.

Jihar Kano ta tsunduma rikita-rikita kan lamarin masarautu tun zamani tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda ya tuɓe rawanin Sarki Sanusi na biyu tare da ƙirƙiran wasu sabbin masarautun masu daraja ta ɗaya, abinda sabuwar gwamnatin NNPP ta Abba Kabir ta rushe kuma ake ta turka-turka a kotuna.

1 thought on “Majalisar jihar Kano ta amince da ƙudirin kafa masarautu masu daraja ta biyu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *