December 7, 2025

Majalisar Dokokin Kaduna za ta binciki gwamnatin El-Rufa’i

IMG-20240417-WA0006.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Mamaki ya mamaye da dama daga cikin masu sharhi kan lamuran siyasar Jihar Kaduna inda a kwana-kwanannan ake neman raba gari tsakanin tsohon gwamnan jihar, Mal. Nasir Elrufa’i da kuma gwamnan jihar mai ci, Mal. Uba Sani.

Idan ba’a manta ba, a ranar 28 na watan da ya gabata ne Mal. Uba Sani, a wani taro da ya gabatar a birnin na Kaduna, ya koka kan irin halin rashin kuɗi da jihar ke fama da shi wanda kuma ake ganin bai rasa nasaba da irin salon mulkin tsohuwar gwamnatin jihar wadda ta ciyo basuka da suka zame alaƙaƙai ga jihar.

A zaman da ta gabatar a jiya Talata, Majalisar Dokokin jihar ta naɗa wani kwamiti mai mambobi goma sha biyu domin ya binciki zarge-zarge da ake ma tsohuwar gwamnatin masu alaƙa da kashe kuɗaɗe a jihar.

Naɗa kwamitin ya biyo bayan wani koke ne da Hon. Yusuf Mugu ɗanmajalisan PDP mai wakiltan mazaɓar Kaura ya gabatar inda a cewarsa haƙƙin al’umman jihar ne su san halin da ake ciki domin samar da shugabanci nagari a faɗin jihar.

Ana sa ran kwamitin zai bibiyi dalilai da ke sa ‘yan kwangila da kamfanoni barin jihar ba tare da sun kammala ayyukan da suka soma a jihar ba wanda haka na nuni da cewa akwai buƙatar bincikan yarjeniyoyi da aka ƙulla da su lokacin bayar da kwangilolin.

Kamar yadda kakakin majalisar ya bayyana a shafukan sada zumuncta, an umurci mambobin kwamitin da su kammala binciken nasu cikin kwanaki 30 daga jiya.

Jama’a da dama da muka zanta da su kan lamarin sun nuna gamsuwa da matakin da majalisar ta ɗauka kan tsohuwar gwamnatin wadda da dama ke ma kallon gwamnati ce wadda ta lalata lamura da dama a faɗin jihar.

Muna sa ran kawo maku sakamokon binciken filla-filla da zaran ya kammala kuma ya iso hannun manema labaru.