Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin kisa ga masu safarar ƙwaya
Daga Sodiqat Aisha Umar
Majalisar dattawan ta amince da ƙudurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar nan, bayan ƙudurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar.
Majalisar ta amince da ƙudurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayyoyi, ƙarƙashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar.
Majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ƙarfafa ayyukan hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa.
To sai dai wasu tsirarun ‘yan majalisar ba su goyi bayan ƙudurin ba, inda Sanata Adams Oshimole ya kasance cikin masu nuna adawa da dokar.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau Jibril ya yi watsi da buƙatar sanata Oshimolen, yana mai cewa ƙorafin sanatan ya saɓa wa dokar majalisar saboda ƙorafin ya zo ne bayan majalisar ta amince da ƙudurin.