Mai ajiyar makullan Ka’aba ya rasu
Daga Abdullahi I. Adam
Bayanai daga Saudiyya sun nuna cewa, Dr. Sakeh bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi wanda shi ne mai kula da makullan Ka’aba ya rasu a safiyar yau Asabar.
Wata sanarwar wadda aka wallafa a shafin Facebook na Inside the Haramain ta nuna cewa mamacin shi ne na 109 a jerin waɗanda su ka taɓa riƙale wannan matsayi tun bayan zamowan birnin Makka ƙarƙashin ikon Musulunci.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da aka kammala ayyukan hajjin bana kuma mahajjata da dama sun soma komawa ƙasashensu, ciki har da Najeriya.