January 13, 2025

Mahara sun kashe wani makiyayi da shanu 50 a Filato

1
image_editor_output_image657502513-1709800988013.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni sa ke fitowa daga Jihar Filato na nuna cewa ƴan bindiga a ranar Talata sun kashe wani makiyayi tare da shanu 50 da kuma tumakai a garin Fanzo dake ƙaramar hukumar Barikin Ladi.

Alhaji Dan-Azumi wanda ya rasa shanu 21 a harin ya tabbatar wa manema labarai cewa an jikkata ƙarin wani makiyayin lokacin da yake kiwo a lokacin.

An ambato shi yana cewa, “Ba zato ba tsammani ƴan bindigar suka farma yankin inda suka fara harbi. Sun kuma kashe ɗaya daga cikin makiyayan suka kuma jikkata wani. Ƴan bindigar sun kuma yi awon gaba da shanu sama da 50. Wasu daga ciki sun mutu a yayin da wasu suka samu raunin harsashi. Hari ne da aka ƙaddamar da shi babu gaira babu dalili.”

“Mu ƴan ƙasa ne masu bin doka  muna kira ga jami’an tsaro dake yankin da su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin gaban shari’a.Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su ƙwato shanun da aka sace.”

Garba Abdullahi, shugaban ƙungiyar, Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN),  wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ya yi kira ga jami’an tsaro da su nemo tare da kamo masu laifin a kuma hukunta su.

1 thought on “Mahara sun kashe wani makiyayi da shanu 50 a Filato

  1. Whawts uup tyis iis somewhat of offf topiic bbut I wwas wanting too knw iif blogs usse WYSIWYG edeitors or if
    yoou have to manually code with HTML. I’m starting
    a blog soon but habe no coding experioence sso I wanted to get guuidance from someone with experience.
    Any help wold bbe enormously appreciated!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *