January 15, 2025

Mahara sun kashe mutane 7 a wani sabon hari a Filato

0
images-2023-11-30T102244.781.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni da ke fitowa daga yankin arewa maso tsakiyar Najeriya na nuni da cewa wasu ‘yan bindiga sun kaddamar da wani mummunan hari a kauyukan Pukah da Pinper da ke ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Harin dai a cewar rahotanni ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan bakwai.

Maharan sun kai harin ne da sanyin safiyar Alhamis, inda suka kashe maza shida da mace daya a yankin Pukah.

Bugu da kari, a yankin Pinper, an bayar da rahoton cewa maharan sun sace tumaki da wasu dabbobin gida.

Wani mazaunin garin Pukah, John Mark, ya tabbatar da mumunan bayanin harin, inda ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka wa al’ummar yankin.

Ya ce, “A yankin Pukah, sun kashe mace daya da maza shida. Amma a Pinper, sun kori tumaki da dama kafin su gudu daga cikin yankin.”

An tuntubi rundunar sojojin da ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a jihar domin jin ta bakinsu.

Sai dai kuma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Kaftin Oya James, mai magana da yawun rundunar, bai bayar da wani bayani game da harin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *