February 10, 2025

Mahaifi Ya Kashe Ƴarsa Saboda Saka Bidiyoyin ‘Da Ba Su Dace Ba’ A Tiktok

4
images-98.jpeg

Daga The Citizen Reports

Wani mutum a Pakistan ya amsa laifin kashe ‘yarsa da aka haifa a Amurka a garin Quetta, lardin Balochistan, bayan ya nuna rashin amincewa da abubuwan da take wallafawa a shafin TikTok.

A cewar rahoton Geo News, wanda ake zargi, Anwar ul-Haq, ya harbe ‘yarsa har lahira a wani titi da ke Quetta a ranar Talata.

A farkon bincike, Haq ya yi ikirarin cewa wani baƙon mutum ne ya aikata kisan.

Sai dai daga baya, yayin binciken ‘yan sanda, ya amsa cewa shi ne ya aikata kisan. “Bincikenmu ya nuna cewa iyalinta na da matsala da irin shigar da take yi, rayuwarta, da kuma abokan zamanta,” in ji jami’in bincike Zohaib Mohsin.

Ya kuma ƙara da cewa, “Mun samu wayarta, amma tana rufe. Muna binciken dukkan bangarorin, ciki har da yiwuwar kisan mutunci ko kuma a ce kisa don mutum ya ɓata wa danginsa suna (wato humanity killing a Turance).”

Rahotanni sun bayyana cewa iyalin sun dawo Balochistan ne kwanan nan bayan shafe kusan shekaru 25 suna zaune a Amurka.

Hukuma ta tabbatar da cewa Haq yana da takardar zama ɗan ƙasa na Amurka. A cewar Geo News, ya shaida wa jami’ai cewa ‘yarsa ta fara wallafa bidiyoyi “marasa kyau” a TikTok tun tana zaune a Amurka, kuma ta ci gaba da hakan bayan sun koma Pakistan.

Haq ya kuma yi ikirarin cewa ‘yarsa ta ci gaba da wallafa abinda ya kira “bidiyoyin batsa” a dandalin TikTok duk da komawa da suka yi Pakistan.

‘Yan sanda sun tabbatar da kama kawun wacce aka kashe dangane da binciken. An gurfanar da Haq da laifin kisa, kuma bincike yana ci gaba.

A halin yanzu, iyalin mamaciyar sun ƙi yin wata magana ga jama’a dangane da lamarin.

A Pakistan, inda TikTok ke da masu amfani da shi sama da miliyan 54, an sha sanya takunkumi kan dandalin saboda damuwa da abun da hukumomi ke cewa bai dace ba.

Kasar mai ra’ayin addini da al’ada na yawan sukar abubuwan da take ganin suna kawo “ɓata tarbiyya” a kafafen sada zumunta.

Kisan mutunci na ci gaba da zama babbar matsala a Pakistan, inda sama da mata 1,000 ke rasa rayukansu kowace shekara a hannun ‘yan uwa ko wasu ‘yan unguwa.

A mafi yawan lokuta, ana kashe su ne saboda ana zarginsu da bata sunan iyali, kamar guduwa da saurayi, wallafa hotuna ko bidiyoyi a kafafen sada zumunta, ko kuma cudanya da maza ta hanyar da ta saɓa wa dokokin al’ada.

4 thoughts on “Mahaifi Ya Kashe Ƴarsa Saboda Saka Bidiyoyin ‘Da Ba Su Dace Ba’ A Tiktok

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *